Home Kasashen Ketare Zai yi shekaru 16 a daure saboda leken asiri

Zai yi shekaru 16 a daure saboda leken asiri

76
0

An yankewa wani tsohon matukin jirgin ruwan Amirka Paul Whelan hukuncin daurin shekaru 16 da aiki mai tsanani, bisa zargin yin makarkashiya a Rasha.

An dai kama shi ne dauke da wani kundin bayanai da jami’an tsaro suka ce yana dauke da wani sirrin kasar, watanni 18 da suka wuce a wani masauki da ke birnin Moscow.

Kotun birnin Moscow ce dai ta kama shi da laifin samun bayanan na musamman.

Whelan, wanda dan asalin kasar birtaniya, Canada da Ireland ne, ya bayyana shari’ar a matsayin salon yaudara, jim kadan kafin a yanke masa hukuncin.

Jakadan Amirka a Moscow John Sullivan, ya yi tir da shari’ar da ya bayyana ba adalci da gaskiya a ciki, yana mai cewa hukuncin zai iya illata dangantakar Rasha da Amirka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply