Home Sabon Labari Zakarun Turai: ƙungiyoyi 16 sun miƙa sunayen ƴan wasansu ga UEFA

Zakarun Turai: ƙungiyoyi 16 sun miƙa sunayen ƴan wasansu ga UEFA

27
0

Hukumar shirya wasanni ta Nahiyar Turai UEFA, ta ce kungiyoyi 16 da suka rage a gasar zakarun Turan sun kammala tabbatar da sauye-sauyen tawagar ‘yan wasansu kafin tunkarar karawar farko ta zagayen ‘yan 16 da za a buga a ranakun 16 da 17 ga watan Fubrairu.

Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na intanet, ranar Laraba.

Kungiyoyin 16 da za su buga wasan zagayen ‘yan 16 sun hada da; Chelsea, Juventus, Real Madrid, Atletico Madrid, Atalanta, Barcelona, Bayern Munich, Dortmund, Paris Saint-Germain, Lazio, Leipzig, Liverpool, Manchester City, Mönchengladbach, Porto da Sevilla.

Daga ranar Talata ne dai aka ba kungiyoyin damar rajistar karin manyan ‘yan wasa uku cikin tawagar da za ta buga masu sauran wasannin da suka rage.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply