Home Sabon Labari Zakarun Turai: Kante zai iya buga wa Chelsea wasa a Munich

Zakarun Turai: Kante zai iya buga wa Chelsea wasa a Munich

108
0

An tabbatar da ɗan wasan tsakiyar Chelsea ya samu lafiyar da zai buga wasan zagaye na 16 bugu na biyu na wasan zakarun turai a Bayern Munich ranar Asabar.

Chelsea dai na fama da matsalar raunin ƴan wasa, inda Frank Lampard ya yi rashin ƴan wasa irin Cesar Azpilicueta, Christian Pulisic da Pedro waɗanda dukkansu suka samu rauni a wasan ƙarshe na cin kofin FA inda ƙungiyar ta yi rashin nasara da ci 2-1 hannun Arsenal.

Chelsea dai ta yi rashin nasara a wasan farko da suka buga da Bayern Munich a London da ci 3-0, kuma duba da raunikan da ƴan wasansa ke fama da shi, Lampard ya ce dole sai ƴan wasan sun yi taka tsantsan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply