Tsohon dan wasan Chelsea Pat Nevin ya yi kira ga manajan kungiyar Frank Lampard da ya sake dawo da Tammy Abraham, Mason Mount da Mateo Kobacic a jerin ‘yan wasan da za su kara da kungiyrar Kransnodar.
A ranar Laraba ne dai Chelsea za ta kece raini da Kransnodar a Rasha, a wasan zakarun Turai na biyu biyu da za su buga a wannan kakar, bayan sun yi kunnen doki da Sevilla a makon jiya.
Chelsea za ta buga wasan ne kuma, bayan kunnen doki babu ci, da ta yi tsakaninta da Manchester United a gasar Firimiya, ranar Asabar.
