Home Sabon Labari Zakarun Turai: Man City na cikin tsaka mai wuya

Zakarun Turai: Man City na cikin tsaka mai wuya

63
0

Ahmadu Rabe

A lokacin da aka fara gasar zakarun nahiyar turai, a ranar Talatar nan, kungiyar Manchester City ta gamu da cikas gabanin tunkarar kungiyar sharktar Donetsk a gobe Laraba.

Mai tsaron baya na kungiyar Jone Stones ne ya ji rauni ya yin da suke atisaye a ranar Talata, kuma an tabbatar zai yi jinyar makonni biyar.

Kocin Manchester City Pep Guadiola na fuskantar matsalar masu tsaron baya. Ko a makon da ya gabata, dan wasa Aymeric Laporte ya tafi jinya.

Yanzu dai Nicolas Otamendi shi daya ne tilo da ya rage a masu tsaron baya na kungiyar.

Masu sharhi da masana harkokin wasanni na ganin kamar da wuya Guadiola ya kai bantensa a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na wannan shekara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply