Home Kasashen Ketare Zakarun Turai: Manchester City ta yi nasara a kotu

Zakarun Turai: Manchester City ta yi nasara a kotu

157
0

A farkon shekarar nan ne hukumar UEFA ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Manchester city tarar zunzurutun kudade da suka kai kimanin fam milyan 25 da kuma haramta wa kungiyar shiga wasannin gasar zakarun turai har na tsawon kakar wasanni biyu a jere, bisa zargin da hukumar take ma ta na karya ka’ida wajen yin cinikayyar ‘yan wasanta.

Hakan ya sa kungiyar ta Manchester City ta daukaka kara a farkon watan Fabrairun shekarar nan a wata kotun da ke sauraron kararrakin wasanni wato CAS .

Sai dai a Litinin din nan ne kotun ta wanke kungiyar Manchester City daga zargin da hukumar take mata, ta kuma bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da shiga wasanni kofin zakarun Turai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply