Home Addini Zakka : Talakawa 1664 sun sami Naira Milyan 164 a Legas

Zakka : Talakawa 1664 sun sami Naira Milyan 164 a Legas

81
0

Wata Gidauniya ta raba Zakka mai suna Zakat and Sadaqat Foundation ta raba Naira Milyan 164 a matsayin Zakka a birnin Legas. Mutane 1664 suka amfana inda wasu suka samu tsabar kudi wasu kuma suka samu kayan aiki da zai taimake su a sana’o’insu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya-NAN- ya ruwaito.

 

Shugaban Gidauniyar Mr Sulaiman Olagunju ya sanar a wurin bikin raba Zakkar na ranar Lahadin nan cewa a wannan shekara ta 2019 sun taba rayuwar jama’a 2,647 ta hanyar rarraba musu Zakka da kudin da suka kai Naira Milyan 220.

Hotan Ayedun Aisha daliba ‘yar aji biyu a kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Akoka Lagos ke karbar keken guragu daga Gidauniyar bayar zakkar a ranar Lahadi.

Shugaban Gidauniyar ya ce da taimakon masu bayar da Zakka sun samu karin Naira Milyan 16 akan kudin da suka samu a shekarar da ta gabata. A don haka ne ya ce a bana sun kara yawan jihohin da suke bayar da Zakka daga jihohi 17 zuwa 21 a wannan shekarar. Sabbin jihohin su ne Kogi da Nasarawa da Zamfara da kuma Naija.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply