Home Addini Zakzaky: Sabon rikici tsakanin ‘yan shi’a da yan sanda a Sokoto

Zakzaky: Sabon rikici tsakanin ‘yan shi’a da yan sanda a Sokoto

96
0

Bayan kammala sallar juma’a ne mabiya mazhabar shi’a a jihar Sakkwato suka soma wani tattaki na sai an saki shugabansu Ibrahim El-zakzaky, inda a kan hanyarsu ta zagaye suka yi wani taho-mugama da jami’an ‘yan sanda a dai-dai shatale-tale na unguwar Dambuwa.

kodayake sun zargi jami’an ‘yan sanda da watsa masu barkonon tsohuwa kana daga bisani suka bude masu wuta da harsasai lamarin da ya sa ake zulumin wani mutum daya ya rasa ransa, wasu mutane goma kuma suka samu munanan raunuka.

Hotan wani wanda ake zargin yan sanda sun raunata a wurin tattakin yan Shi’a a Sokoto a ranar Juma’a

To sai dai da DCL Hausa ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ASP Muhammad Sadiq Abubakar ya musanta jikkata wani daga cikin ‘yan shi’ar. Ya ce sun dai kawai watsa masu barkonon tsohuwa ne amma babu batun hallaka wani da harsashi.

Yan shi’ar dai na korafin a saki shugabansu Ibrahim El Zakzaky tunda har an saki Kanar Sambo Dasuki mai murabus da Omoyele Sowore da gwamnatin Nijeriya ta yi a cikin makon nan. Yan shi’ar na ganin tunda har an saki wadannan mutane guda biyu to ya kamata a saki shugabansu wanda ya kasance mutum na uku a cikin fitattun mutane uku da gwamnati ke tsare da su a mulkin shugaba mai ci Muhammadu Buhari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply