Home Sabon Labari Zaman Aubameyang a Arsenal ya zo karshe?

Zaman Aubameyang a Arsenal ya zo karshe?

53
0

Dan wasan gaban Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, ya ce yanke shawara kan ko zai tsawaita zaman sa a kungiyar, wani muhimmin abu ne ga rayuwar sa ta kwallon kafa.

Wa’adin dan kasar Gabon, mai shekaru 30 a duniya, a kungiyar dai zai kare ne a cikin watan Yunin shekarar 2021

Aubameyang ya shaidawa Telefoot cewa har yanzu bai samu wani sabon tayi ba, amma ya yi magana da kungiyar watannin da suka gabata.

Ya ce batun tsawaita yarjejeniyar shi ne babban abu a harkar sa, saidai ya ce yana so ya zama mai gaskiya ga kowa.

Aubameyang ya ciwa Arsenal kwallaye 61 a wasanni 97 da ya bugawa kungiyar tun da ya bar Borussia Dortmund a shekarar 2018.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply