A cikin shirin na wannan makon, za ku ji labarin wani dan kasuwa da ya fara kasuwanci da Naira 100 a matsayin jari, amma yanzu kuma ya mallaki shagon kansa a cikin garin Kafur na jihar Katsina. Muna dauke da tattaunawa da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari kan matakan da ya kamata a dauka kan masu ba ‘yan bindiga bayanai, da akafi sani da informants. A karamar hukumar Batagarawa kuma wata babbar jami’ar gwamnati ta ba mu wani muhimman sako.
Latsa alamar sauti da ke kasa domin sauraron shirin
