Latsa kasa domin sauraron shirin
A shirin namu na wannan makon iyayen daliban da suka kubuta daga hannun ‘yan bindiga a jihar Katsina na ci gaba da murnar haduwa da ‘ya’yansu. Muna dauke da rahoto na musamman. A garin Dutsinma mun hadu da wata matashiya wace ta kirkiro wa kanta wata sana’a mai kawo kudi a cikin gidan mahaifinta. Muna kuma da wani babban sako da mutanen garin Daura suka bai wa tawagarmu.
