Home Sabon Labari ZAMBA CIKIN AMINCI: HUKUMA TA MUSANTA ZARGIN KARKATAR DA KUDIN MAHAJJATA

ZAMBA CIKIN AMINCI: HUKUMA TA MUSANTA ZARGIN KARKATAR DA KUDIN MAHAJJATA

81
0

Daga Saleem Ashiru Mahuta/NIB

 

Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Kano dake Arewa Maso yammacin Nijeriya, ta musanta zargin da ake mata na karkatar da kudaden da aka aikawa mahajjatan jihar domin Hadaya a yayin aikin Hajjin bana.

Da yake jawabi ga Manema Labaru a Jiya Talata, Shugaban Hukumar Mohammad Dambatta, ya wanke hukumar daga zarge-zargen, inda ya bayyana cewa Hukumar bata nemi ko amsar kudin wani daga cikin mahajjatan domin hadaya ba.

Ya kuma tabbatar da cewa, Bankin Musulunci na Jaiz ne kadai Hukumar aikin Hajji ta Kasar NAHCON da wasu jami’an Kasar Saudiyya aka baiwa izinin amsar kudaden hadayar, inda ya bayyana cewar Hukumar ba ta da hannu wajen rike kudaden da aka aika masu.

Mahajjatan daga Nijeriya dai na cigaba da kokawa kan rashin basu kudin su na Hadaya a hannu tun bayan da Hukumar NAHCON ta bayyana rage masu kimanin Naira dubu 51, inda wasu Jihohin suka ki mayarwa da mahajjatan kudaden da nufin za a biya masu kudin hadaya idan anje kasa mai tsarki.

Source: Guardian

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply