Daga Abdullahi Garba Jani
Gwamnan jihar Zamfara Alh Bello Matawalle ya amince da nadin Alh Abubakar Gado Maigari a matsayin sarkin Maru na jihar.
Bayanin nadin na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin gwamnan jihar Barr. Mahdi Aliyu Gusau.
Nadin nasa ya biyo bayan tsige sarkin Maru da aka yi, bisa zargin samunsa da aka yi da hannu a kashe-kashe da sace-sacen shanu a jihar.
Kafin nadin Alh Abubakar Maigari, babban hakimi ne a masarautar Maru, sannan ya rike sakatarrn masarautar na tsawon lokaci.
Takardar ta bukaci sabon sarkin da ya gudanar da mulkinsa cikin adalci da rikon amana.
