Home Sabon Labari Zamfara: An samu Sarki da Hakimi da hannu dumu-dumu a rikicin jihar

Zamfara: An samu Sarki da Hakimi da hannu dumu-dumu a rikicin jihar

66
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Gwamnan jihar Zamfara Alh Bello Matawalle ya amince da tsige Sarkin Maru Alhaji  Abubakar Chika da Hakimin garin Kanoma Alhaji Lawal Ahmad.

A wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin gwamnan jihar Barista Mahdi Aliyu Gusau, ta ce gwamnan ya amince da tsige su daga mukamansu ba tare da bata lokaci ba.

A watan Yunin da ya gabata ne aka dakatar da mutanen 2 daga mukamansu, biyo bayan zanga-zangar da mutanen da suke mulka suka yi na zargin hada hannunsu a satar shanu da kashe-kashen mutanen jihar.

Daga nan aka kafa wani kwamiti karkashin jagorancin tsohon babban sufeton ‘yansanda na kasa MD Abubakar don bincika zarge-zargen.

A cikin aikin da kwamitin ya aiwatar ne ya gano cewa suna da hannu dumu-dumu a ciki, har ma kwamitin ya ba da shawarar a tsige su daga mukamansu.

Hakimin Kanoman da aka tsige su tare da Sarkin na Maru, shi ma cikin masarautar Sarki Alhaji Abubakar Chika ya ke.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply