Home Sabon Labari Zamfara:  an yi gwanjon kadarorin gwamnati na kudi kimanin naira milyan 282.5.

Zamfara:  an yi gwanjon kadarorin gwamnati na kudi kimanin naira milyan 282.5.

71
0

Daga Rahama Ibrahim Turare

 

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya karbi cakin kudi (cheque)na kimanin Naira milyan   282.5 daga hukumar dake kula da gwanjon kadarorin gwamnati,  AMCON.  Kudaden dai rara ce daga gwanjon kayayyakin gwamnati da aka yi.

 

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN)ya ruwaito cewa  hukumar -AMCON- tayi gwanjon kaddarorin gwamnati masu tarin yawa wadanda suka shafi abubuwan hawa masu amfani, a lokutta daban-daban a karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari. Kuma  wannan kudin da aka samu yanzu na da alaqa da kudin kadarorin gwamnati da a ka sayar a zamanin tsohon gwamnan.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle

Mai magana da yawun gwamnan jihar Malam Yusuf Idris ya bayyana cewa, gwamna Matawalle ya karbi cakin kudin daga jami’in hukumar AMCON Mr.Sa’ad Ahmad tare da shugaban kula da bangaren shari’a na hukumar Mr. Albert Nwanzie. Ya kara da cewa ‘cakin’ kudin na dauke da kwanan wata 16 ga watan Agusta 2019.

 

Gwamnan jihar ta Zamfara dai ya sha alwashin ci gaba da bibiyar duk wasu kayan gwamnati da aka yi gwanjonsu a shekarun baya, har sai an tabbatar da an karbo kudadensu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply