Home Labarai Zamfara: Kungiyoyin Farar Hula sun nemi kotu kar ta sauya hukuncin ta

Zamfara: Kungiyoyin Farar Hula sun nemi kotu kar ta sauya hukuncin ta

62
0

Wasu gamayyar kungiyoyin farar hula sun yi kira ga kotun kolin Nijeriya da kar ta sauya hukuncin da ta yanke a ranar 24 ga watan Mayun bara kan zaben gwamnan jihar Zamfara.

Kungiyoyin sun ce duk wani yinkuri na sauya hukuncin ba zai haifar da da mai ido ba, ga jama’ar jihar wadanda suka samu gamsuwa ga gwamnatin jihar mai ci.

Yanzu haka dai batun sake shigar da kara da jam’iyyar APC da Abdulaziz Yari suka yi a kotun kolin, shi ne batun da ke daukar hankali a jihar ta Zamfara.

Jam’iyyar na neman kotun kolin ta janye hukuncin da ta yanke a ranar 24 ga watan Mayun bara, wanda ya soke dukkan zabukan da APC ta samu nasara a babban zaben da ya gabata.

A wani yinkurin hadin gwiwa da kungiyoyin suka yi, sun bukaci kotun ta yi watsi da bukatar ta APC musamman ganin yadda jama’ar jihar ke da cikakken kwarin gwiwa ga gwamnati mai ci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply