Home Sabon Labari Zamfara: Sanata Marafa ba dan APC bane-Kungiya

Zamfara: Sanata Marafa ba dan APC bane-Kungiya

75
0

Wata kungiyar siyasa a jihar Zamfara mai suna “Zamfara State APC Concern Citizen” ta yi kira ga Sanata Kabiru Marafa da ya janye jikinsa daga tsoma kansa a harkokin siyasar APCn jihar Zamfara.

Kungiyar ta ce tsoma hannun da Kabiru Marafa ya ke yi na kawo rudani da matsaloli ga jam’iyyar wanda tace tuni jam’iyyar ta kore shi bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-kasa.

Sakataren kungiyar Comrade Aliyu Ibrahim Marafa ya yi zargin kwangilar da aka ba Sanata Marafa na ya kawo sabon hargitsi a jam’iyyar ba za ta sake yin tasiri ba a wannan karon.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply