Home Sabon Labari Zamfara: Sanata Marafa da Tsohon Gwamna Yari na tattaunawar sulhu

Zamfara: Sanata Marafa da Tsohon Gwamna Yari na tattaunawar sulhu

83
0

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara a jam’iyyar APC Aminu Sani Jaji ya ce an shawo kan duk matsalolin da suka sa jam’iyyar ta sha kaye a zaben da ya gabata.

Aminu Jaji na mai da martani ne kan wata takara da ake alakantawa da sakataren watsa labaran jam’iyyar na jihar mai cewa an gan shi ya gana da tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari a matsayinsa na wakilin kungiyar G8.

Sakataren watsa labaran jam’iyyar Shehu Isah a wata ganawa ya ce Abdul’aziz Yari da wasu jiga-jigan kungiyar G8 sun gana a Abuja don dinke barakar da aka samu. Kazalika shugaban jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara Alhaji Lawal Liman ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya-NAN- cewa wannan sulhu abu ne mai kyau ga ci gaban jam’iyyar.

Isah Shehu ya ce daga cikin wadanda suka halarci taron hada Sanata Kabiru Garba Marafa, Dauda Lawal, Ibrahim Wakala, Mahmud Shinkafi da Aminu Sani Jaji sa dai sauransu.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja, Aminu Sani Jaji ya ce ya halarci taron ne a kashin kansa, ba wai dan wani rukuni ba.

Takaddamar siyasa a tsakanin bangaren su Sanata Kabiru Marafa da tsohon Mataimakin Gwamna Ibrahim Wakkala da sauransu da kuma bangaren Gwamna Yari a watan Satumbar 2018 ita ce ta ruru har ta yi sanadiyyar jam’iyyar PDP ta samu mulki a jihar Zamfara. Sai kuma ga shi yanzu wadannan ‘yan siyasa na neman dinke barakar da ke tsakaninsu bayan kowanensu ya rasa samun madafun iko.

 

Ya kuke kallon wannan yunkuri na sasanci?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply