Home Lafiya Zamfara: Sojojin Saman Nijeriya na duba lafiyar mutanen da rikici ya shafa

Zamfara: Sojojin Saman Nijeriya na duba lafiyar mutanen da rikici ya shafa

95
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Rundunar sojin saman Nijeriya na gudanar da shirin kula da lafiya kyauta ga wadanda rikici ya daidaita su 3,000 a jihar Zamfara. Daraktan hulda da jama’a na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola a cikin wata takarda a Abuja ya ce wadanda suka amfana da shirin sun fito daga kauyen Kanoma na karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

 

Daramola yace hakan ya biyo bayan umurnin da babban hafsan sojin sama na kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya bahyar na kai dauki ga al’ummomin da ke bukatar hakan a wasu sassan jihar Zamfara.

 

Sojojin sama a lokacin da suka duba lafiyar jama’a kyauta a jihar Benuwai

Kamfanin Dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito cewa, daga cikin shirin kula da lafiyar da za a gudanar kyauta a jihar har da gwaje-gwajen ciwuka daban-daban, samar da gilassan inganta gani ga mutane sama da 1,000, samar da gidan sauro ga mata masu juna biyu da sauransu.

 

Gwamnan jihar Zamfara yi godiya da son-barka ga rundunar sojin bisa wannan tallafi da ta ba mutanen jihar

 

Wannan  dai na cikin ayyukan jin-kai, Corporate Social Responsibility, da rundunar sojin sama ta kewa jama’ar jihar Zamfara a sakamakon aikin da take yi na samar da tsaro a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply