Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne, a hirarsa da DCL Hausa, inda ya ce bai yi musu ga cire tallafin man fetur a Nijeriya ba, amma abin tambayar shine inda kuɗin suke tafiya.
A cewarsa al’ummar Nijeriya ba suga amfanin cire tallafin man fetur ba, saboda basusan inda kudadensu ke tafiya ba, in akai duba da halin matsi da talakan Nijeriya ke ciki a wannan lokaci kuma duk wanda ya saci kuɗin al’umma sai ya maido.
Atiku ya yi zargin cewa ba a taɓa gwamnatin da ake sata kamar ta shugaba Tinubu ba, inda ya ce duk tsare-tsaren da gwamnatin ke yi domin nunawa al’umma tana tare da su yaudara ce, hakan ya faru ne saboda zaɓe na ƙaratowa.
A cewarsa tunda aka dawo dimukraɗiyya a Nijeriya, ba a taɓa samun gwamnatin da ta kula da al’umma suka ji daɗinta kamar lokacin da yana mataimakin shugaban Nijeriya a jam’iyyar PDP ba.
Da ake tambayarsa kan batun tallafin karatun ɗalibai da Tinubu ya ba da umurnin a karkatar da kuɗaɗen da EFCC ta ƙwato ga asusun ba da lamunin karatun ɗalibai (NELFUND), Atiku ya ce yaudara ce domin tun farkon gwamnatin mai yasa bai yi haka ba sai da ake fuskantar zaɓe.
Atiku ya kuma ƙalubalanci gwamnatin Tinubu kan matsalar tsaro, inda ya ce rashin biyan jami’an tsaron Nijeriya haƙƙoƙinsu na taimakawa wajen kalubalen da ke faruwa.
Ya kara da cewa akwai ƙarancin jam’ian tsaro da Nijeriya ke fama da shi, domin a cewarsa akwai kasashe da dama da basukai Nijeriya tattalin arziki ba amma suna da isasssun jami’an tsaro, kuma lallai akwai bukatar karin jami’an tsaro a Nijeriya.
