DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBabban Labari Zan sanya kayan Akwete idan aka sake zaɓar mijina a 2027 –...

Zan sanya kayan Akwete idan aka sake zaɓar mijina a 2027 – Oluremi Tinubu

Uwargidan shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa za ta riƙa sanya kayan gargajiyar Akwete idan aka sake zaɓar mijinta, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin shugaban ƙasar na wa’adi na biyu.

Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da ta kai ziyararta ta farko zuwa ƙauyen haɗin gwiwar masu sana’ar saƙar Akwete da ke jihar Abia, inda ta kuma sanar da bayar da tallafin Naira biliyan biyu domin farfaɗo da sana’ar saƙar kayan Akwete.

Ta ce idan Allah ya sake ba mijinta damar shugabantar Nijeriya a karo na biyu, za ta sanya riga da zani da aka ƙera da kayan Akwete, saboda ta yaba da laushin kayan da kuma yadda suke da sauƙin amfani da su.

Uwargidan shugaban ƙasar ta yaba wa mata masu sana’ar saƙar Akwete bisa jajircewarsu da ƙoƙarinsu na kare wannan sana’a ta gargajiya, tare da ci gaba da gadar da ita daga tsara zuwa tsara.

Ta bayyana cewa ta ga yadda wasu matasa ke koyon sana’ar daga iyalansu, lamarin da ke nuna yadda ake gadar da wannan sana’a ta gargajiya daga iyaye zuwa ’ya’ya.

Oluremi Tinubu ta kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su riƙa amfani da kayan gargajiyar Igbo da ake ƙera su da Akwete, domin hakan zai taimaka wajen tallafa wa masu saƙa da kuma bunƙasa sana’o’in hannu na cikin gida.

Ta ce ziyarar da ta kai ƙauyen masu saƙar Akwete ba ta kasance cikin wani tsari na musamman ba, domin ta je ne da niyyar ganawa da matan da ke gudanar da sana’ar, tare da jin labarinsu da fahimtar irin ƙalubalen da suke fuskanta.

Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma bayyana godiyarta ga Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, inda ta bayyana shi a matsayin mutumin kirki. Ta ce a baya ta taɓa tuntuɓar matar gwamnan domin neman ƙarin bayani game da sana’ar saƙar Akwete.

Ta ƙara da cewa, duk da jinkirin da aka samu kafin ziyarar ta tabbata, ta gode wa Allah da ya ba ta damar zuwa jihar Abia domin ganawa da mata masu wannan sana’a da kuma ganin yadda ake gudanar da ita.

A ƙarshe, Oluremi Tinubu ta jaddada muhimmancin tallafa wa kayayyakin da ake ƙera su a cikin gida, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare al’adun gargajiya, bunƙasa sana’o’in hannu da kuma inganta rayuwar masu sana’ar saƙa, musamman a yankunan karkara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata