Wasu rahotanni da ke fitowa daga garin ‘Yantumaki karamar hukumar Danmusa jihar Katsina, sun ce wasu mutane da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun shiga garin sun yi harbe-harben bindiga har sun tafi da mutane 3.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mutanen sun isa garin ne da misalin karfe 1 na dare a ya yi suka shiga gidan Alhaji Mansur Yusuf wanda makwabcin Hakimin garin ne da aka kashe a kwanakin baya, suka yi awon-gaba da shi da ‘yar sa.
Majiyar ta ce wannan lamarin ya harzuka mutanen garin sun fito bakin titi suna zanga-zanga tare da kona tayoyi a kan titi, suna zargin kamar akwai sakacin gwamnati a lamarin.
Har ya zuwa wannan lokacin, rundunar ‘yansandan jihar Katsina ba ta ce uffan ba a kan batun.

Ai duk yanxu baxata CE komi ba amma zata ce