Dubunnan jama’a ne suka gudanar da zanga-zangar lumana a fadin Amirka a rana ta takwas bayan mutuwar Afiriken dan Amirkan nan George Floyd a hannun ‘yan sanda.
Daya daga cikin manyan zanga-zangar da aka yi ita ce wadda aka gudanar a garin marigayin na Houston da ke jihar Texas wadda har ‘yan uwan sa suka shiga.
Mutane da dama dai sun ki yin biyayya ga dokar hana fita da aka sanya a birane da dama, biyo bayan rikicin da ya barke da kuma satar shaguna da aka gudanar a daren ranar Litinin.
A tsakiyar Birnin Washington DC ‘yan sanda sun rika harba barkonon tsohuwa har zuwa tsakar dare.
An kuma jige sojoji a kan titunan babban birnin kasar yayin da jirgi mai saukar angulu ya rika shawagi kan masu zanga-zangar da suka doshi fadar White House.
Mutuwar Floyd dai, ta kara ririta wutar nuna bacin rai kan yadda ‘yan sandan Amirka ke kashe bakake da kuma nuna masu kyama.
