Home Sabon Labari Zanga-Zangar ‘Yan Shi’a: Buhari ya bayar da umarni ga jami’an tsaro.

Zanga-Zangar ‘Yan Shi’a: Buhari ya bayar da umarni ga jami’an tsaro.

175
0
  1. Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya Mohammed Abubakar Adamu ya shaida wa ‘yanjarida a fadar shugaban kasa cewa, Shugaba Buhari ya ba su umarni su tabbatar sun kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da ‘yan Shi’a ke ci gaba da zanga zanga a Abuja.

Shugaban ‘yansandan ya shaida wa shugaban Nijeriya cewa ‘yansanda na iyakar kokarinsu wurin ganin ba su bar wata kungiya ta muzgunawa sauran ‘yan kasa ba kuma za su ci gaba da kokarin kare rayukan jama’a musamman a wannan lokaci.

Zanga zangar da ‘yan Shi’a suka yi a ranar litinin don a fito musu da jagoransu, ta yi muni inda ‘yansanda suka rasa ran wani babban jami’insu, ‘yanjarida kuma suka rasa wata ‘yarjarida ta gidan talabijin na Channels ya yin da su kuma yan Shi’a rahotanni suka ce sun rasa mutune 11.

Wannan muni da zanga zangar ta yi ne ya sa Shugaba Buhari a jiya litinin ya kira gaba daya shugabannin hukumomin tsaro na kasa don duba yadda za a iya dakile barkewar rashin doka da oda a kasar nan.

 

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply