Home Sabon Labari Zargin Amfani da Kudin Haram: kotu ta gindawa Maurice Iwu sharuddan samun...

Zargin Amfani da Kudin Haram: kotu ta gindawa Maurice Iwu sharuddan samun beli

69
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Wata kotu a Legas da ke Kudancin Nijeriya ta ce za ta ba da belin tsohon shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Maurice Iwu bisa sharadin mallakar naira bilyan daya ga duk mai son amsarsa beli.
Kotun ta ce mutane biyu take son su tsaya wa Mr. Iwu kuma kowanensu sai ya mallaki gida a Legas. Sannan kotu ta ce mutane biyun kowanensu sai ya zo kotu ya nuna akwai akalla Naira Bilyan Daya a cikin asusunsa na banki.

Hukumar-EFCC- ta damke Maurice Iwu ne bisa zargin boye kudin haramun da suka kai Naira Bilyan 1.23

Kazalika, an bukaci mutane biyun da aka amince su tsaya masa da su mika kananan hotunansu guda bi-biyu.

Kafin Mr Iwu ya cika wadannan sharuda za a ci gaba da tsare shi har sai ya cika sharuddan ba da belin da aka gindaya ma sa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply