Home Labarai Zargin Fyade: Akpabio ya karyata zargin shugabar NDDC Nunieh

Zargin Fyade: Akpabio ya karyata zargin shugabar NDDC Nunieh

104
0

Ministan yankin Neja Delta Godswill Akpabio ya karyata zargin da tsohuwar babbar daraktar hukumar ci gaban yankin Neja Delta NDDC Joi Nunieh ke yi masa.

A wata zantawa da ta yi da ‘yan jarida baya-bayan nan, Nunieh ta zargi Akpabio da cin zarafinta, cin hanci da kuma karyata ka’idojin aiki da sauran zarge-zarge.

Saidai a cikin wata sanarwa da ministan ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Aniete Ekong, ya bayyana zargin a matsayin karya da kuma son bata masa suna.

Sanarwar ta ce babu wani lokaci da ministan ya taba yinkurin yin fyade ko saduwa da Nunieh ko kuma wata ma’aikaciyarsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply