Home Labarai Zargin lalata da ɗalibai: kwalejin Ibadan ta kori malami

Zargin lalata da ɗalibai: kwalejin Ibadan ta kori malami

227
1

Shugabannin Kwalejin kimiyya da fasaha ta Ibadan sun kori wani malaminsu Kelani Omotosho, kan zargin sa da yin lalata da wata ɗaliban.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da maga-takardan kwalejin Mrs Modupe Fawale ta fitar a Ibadan ranar Asabar.

Shugabannin sun bayyana cewa an kori malamin ne bisa shawarar kwamitin bincike da aka kafa kan sa, saboda barinsa zai ɓata sunan kwalejin.

Shi dai Kelani Omotosho, ya fito daga sashen koyar da tsare-tsaren birane da ke kwalejin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply