Home Labarai Zazzau: An sake sabon-lale wajen zaben sarki

Zazzau: An sake sabon-lale wajen zaben sarki

257
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce masu zaben sarki a masarautar Zazzau ta jihar na can sun dukufa don sake bin hanyoyin zaben sarki.

Sakataren gwamnatin jihar Balarabe Abbas Lawal a cikin wata takarda daga mai magana yawun gwamnan Kaduna, ya ce gwamnatin jihar ta umurci masu zaben sarkin da su sake sabon-lale na zaben sarkin, biyo bayan soke wancan tsohon tsarin da gwamnati ta yi da ya fitar da masu neman sarautar su 2.

Yanzu haka dai masu zaben sarkin na can sun saka lalube domin tantance masu neman sarautar su 13.

Takardar ta ce da zarar sun kammala aikin da aka ba su, za su mika rahoton ga gwamnan jihar Malam Nasir El Rufa’i.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply