Home Labarai Zazzau: El-rufai na ganawar sirri da masu zaben Sarki

Zazzau: El-rufai na ganawar sirri da masu zaben Sarki

384
0

Masu zaben Sarkin Zazzau yanzu haka suna ganawa ta musamman da gwamna El-Rufa’i a gidan gwamnatin jihar na Sir Kasim Ibrahim.

Jaridar Daily Trust ta rawaito, cewa ‘ya’yan sarki 11ne suka nuna aniyarsu ta son su gaji marigayi Sarki, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata.

Tuni dai dama masu zaben sarki a masarautar ta Zazzau suka gabatar da sunayen mutane uku ga gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da ke son sarautar ta Sarkin Zazzau.

Ga ma sunayensu da adadin makin da kowa ke dashi.
Sunayen sune:

Alhaji Bashir Aminu, Iyan Zazzau, wanda ya ci maki 89.

Alhaji Muhammed Munnir Jafaru, Yariman Zazzau, with 87.

Alhaji Aminu Shehu Idris, Turakin Karamin Zazzau, wanda ya ci maki 53.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply