A daidai lokacin da ake shirin buga wasan hamayya na birnin Madrid, mai horaswar Real Madrid Zinedine Zidane ya amince cewa Atletico Madrid na kan ganiyar lashe kofin La Liga a wannan kakar.
Da ake ganawa da shi a ranar Juma’a Zidane ya ce an fi kyautatawa Madrid zaton ɗaukar kofin duba da irin jajircewar da suke nuna wa a fagen daga.
Za dai a gudanar da wasan ne a ranar Asabar ɗin nan, saidai masu hasashe na ganin Real Madrid za ta iya yin nasara a wasan duk da wasanni 10 da Atletico ta yi ba tare da ta yi rashin nasara ba.
