Rahama Ibrahim Turare/Banye
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta ce a ranar Lahadi mai zuwa 15.09.2019 za a binne gawar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe wanda ya rasu a ranar Juma’a. Sashen Hausa na DW ya bada labarin cewa gwamnatin kasar ta bukaci iyalan Robert Mugabe su zabi inda za’a binne marigayin.
Jim kadan bayan sanar da mutuwar ta Mugabe shugaban Ƙasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya bayyana marigayin a matsayin gwarzo kuma mai kishin ƙasa.
Mugabe dan shekara 95 ya mutu da safiyar ranar Juma’a a kasar Singapore inda yake karbar magani tun watan Afrilu
Yayin da yake yiwa ƴan kasar jawabi, Shugaba Mnangagwa ya bayyana ranaku domin yin makoki a kasar har zuwa lokacin da za’a binne gawar Mugabe.
Ya ce “bayan zaman tattaunawa da jam’iyyar mu ta ZANU-PF ta yi, ta ba shugaba Mugabe matsayin gwarzon ɗan kasa, wanda ya cancanci wanannan matsayi”.
Ya kara godewa gwamnatin kasar Singapore bisa ga kulawa da suka yi da lafiyar shugaba Mugabe har zuwa mutuwar shi.
A ci gaba da tunawa da shugaba Mugabe, Mista Mnangagwa ya jinjinawa tsohon shugaban kasar akan irin ci gaban da ya kawo da sadaukarwar sa ga Zimbabwe.
