Gwamnatin ƙasar Zimbabwe za ta mayarwa turawa ƴan ƙasashen waje gonakinsu da aka ƙwace masu da ƙarfin tuwo kimanin shekaru 20 da suka gabata.
Ministan Kuɗin ƙasar Mthuli Ncube ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Harare babban birnin ƙasar.
Dubban manoma turawa ne dai gwamnatin ƙasar ta karɓe wa gonakinsu a shekarar 2000 zuwa 2001.
Lamarin da ya haifar wa ƙasar ta Zimbabwe koma bayan tattalin arziƙin, kuma ya lalata alaƙa tsakanin ƙasar da ƙasashen yamma.
