Home Labarai Zulum ya bayyana dalilan da suka kawo tsaiko a yaki da Boko...

Zulum ya bayyana dalilan da suka kawo tsaiko a yaki da Boko Haram

185
0

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babana Umara Zulum ya bayyana dalilan da suka sanya aka kasa kawo karshen yaki da kungiyar mayakan Boko Haram.

A cikin wata hira da Zulum din ya yi da sashen Hausa na BBC yace “matukar ba a tayar da mayakan kungiyar Boko Haram daga Tafkin Chadi da ma wadanda suke cikin dajin Sambisa ba, to yakin ba zai kare ba.

Ya kara da cewa matukar ana so a yi nasara wajen kawo karshe rikicin dole sai an samu hadin kai daga kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya.

Ya bayyana cewa yana nan akan bakansa na cewa sojoji na yi masa zagon-kasa wajen yakin da ya ke yi da kungiyar ta Boko Haram.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply