Gwamnan jihar Borno Farfesa Umara Babagana Zullum ya rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomi 27 na jihar.
Daga cikin sabbin shugabannin akwai farfesoshi 2.
Zulum ya rantsar da su a jiya (Laraba) a dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar.
Farfesa Adamu Alooma da zai shugabanci karamar hukumar Damboa, sai kuma Farfesa Ibrahim Bukar da zai shugabanci karamar hukumar Gwoza, dukkanin su daga Jami’ar Maiduguri.
