Home Labarai Zulum ya ware bilyan 12 don biyan giratutin tsoffin ma’aikata

Zulum ya ware bilyan 12 don biyan giratutin tsoffin ma’aikata

54
0

Gwamnan jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum ya sanar da cewa ya ba da kudi Naira bilyan 12 don biyan ma’aikata 4,862 da suka ajiye aiki a jihar.

Yace za a biya bashin tsoffin ma’aikatan ne wadanda suka ajiye aiki tun daga 2013 zuwa 2017.

Da ya ke kaddamar da ba da chakin kudin a birnin Maiduguri, gwamna Zulum yace gwamnatin jihar ta samo kudin ne ta hanyar bashin banki.

Gwamnan ya tunaso cewa ko a watan Yunin 2019, gwamnatin jihar ta ba da kudi Naira bilyan 2 don biyan kananan ma’aikata 1,684 da suka ajiye aiki daga 2013 zuwa 2019.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply