Gwamnan jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum ya amince da daukar karin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya 594 a jihar.
Kamar yadda yace, za a dauki likitoci 84, nas-nas da ungozoma 365 sai masu harhada magunguna su 45 da karin sauran jami’an kiwon lafiya 100.
Da ya ke magana a wajen taron masu ruwa da tsaki kan kiwon lafiya, gwamna Zulum ya ce idan aka yi haka, za a samu sauki sosai game da sha’anin kiwon lafiya a jihar.

Allah yabashi nasara
Allah yataimaka allah yasa asamu nagari baburigubiba