Home Labarai Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomi

Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomi

149
0

Hukumar zabe ta jihar Borno, ta sanar da ranar 28 ga watan Nuwambar wannan shekara, 2020 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

A watan Yunin da ya gabata ne hukumar ta tsara gudanar da zaben, amma aka dage shi saboda cutar corona.

Da ya ke karin haske ga manema labarai a birnin Maiduguri, shugaban hukumar, Alhaji Abdu Usman, ya ce an fara gudanar da dukkanin tsare-tsaren zaben.

Ya ce hukumar za ta tabbatar da an gudanar da sahihi kuma karbabben zabe a daukacin kananan hukumomi 27 na jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply