Home Labarai Zuwa aiki a makare shima kwarafshin ne – Magu

Zuwa aiki a makare shima kwarafshin ne – Magu

59
0

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC Ibrahim Magu ya bayyana rashin zuwa aiki kan lokacin a matsayin cin hanci da ya ce wajibi ne a ga bayan sa.

Da yake magana lokacin wani gangamin yaki da cin hanci da hukumar ta shirya hadin gwiwa da shirin matasa masu yiwa kasa hidima NYSC a Abuja, ya ce abun takaici ne ka ga har karfe 10:30am na safe amma bai wuce kashi 10 na ma’aikata ne suka zo aiki a sakatariyar gwamnatin tarayya ba.

Ya ce wannan cin hanci da ya zama wajibi a yake shi.

A nasa bangaren ministan matasa Sunday Dare ya yi kira ga matasan da su ci gaba da wannan kokari na yaki da cin hanci.

Ya ce su ci gaba da yada sakonnin yaki da cin hancin a ko ina, domin kuwa idan har aka ga bayan sa, to goben su ce za ta yi kyau.

Wannan gangami dai, matasa masu yiwa kasa hidima da ke yaki da cin hanci ne suka shirya shi tare da gudunmuwar wasu matasan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply