DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ruftawar gini ta yi ajalin mutane a sansanin ‘yan gudun hijira na Borno

-

 

Google search engine

Rahotanni daga birnin Maiduguri na cewa mutane 7 sun mutu a sakamakon faduwar gini a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri na jihar Borno.

Jami’an kungiyar Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa wani aji ne ya fado kan wasu mutane da ke kwana a ciki sanadin ruwan sama a garin Munguno.

Bayanai sun ce ginin ya fado ne da misalin karfe 7 da rabi na safiyar yau, kuma nan take mutane 7 suka ce ga garin ku nan.

Wasu jami’an lafiya sun tabbatarwa manema labarai cewa akwai mutane fiye da 20 yanzu haka da ke kwana a babban asibitin garin Munguno suna karbar magani bayan raunukan da suka gamu da su.

Garin Munguno da ke da nisan kilomita 85 zuwa birnin Maiduguri na da ‘yan gudu hijira fiye da dubu 40 wadanda suka gujewa ta’addancin Boko Haram daga garuruwan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon Gwamnan jihar Kwara Cornelius Adebayo ya rasu

Tsohon Gwamnan jihar Kwara kuma Ministan Sadarwa na baya, Cornelius Adebayo, ya rasu yana da shekara 84 a Abuja da safiyar Laraba nan. Babban dansa Oluwasegun,...

An karrama ma’aikacin gwamnatin Jigawa a Saudiyya bisa dawo da kuɗin da ya tsinta

Wani ma’aikacin gudanarwa a Saudiyya, Muhammed Salalah, ya mika kwafin Alkur’ani Mai Tsarki ga Daraktan Rediyon Jigawa, Malam Isma’il Babura, a matsayin kyauta mai daraja...

Mafi Shahara