DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba mu da shirin kara farashin man fetur-IPMAN

-

Google search engine

Kungiyar dillalan
man fetur ta IPMAN ta musanta labarin da ke cewa tana shirin kara farashin man
fetur.

Shugaban kungiyar
reshen jihar Enugu Mr Chinedu Anyaso ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa
da manema labarai, yana mai cewa akwai bukatar jama’a su yi watsi da wannan
labari.

Ya ce basu sami wani umarni ko shawarar kara
man fetur daga kamfanin mai na kasa NNPC ba don haka babu wani dalili da zai
sanya su kara farashin man fetur din a halin yanzu.

Bayanin nasa na zuwa ne dai-dai lokacin da jama’a
suka fara sayen man fetur da yawa don adanawa, saboda tsoron karin farashin man
kamar yadda ake yadawa.

 Ya ce a maimakon kara farashin man yana da hasashen
cewa za’a sauke farashi ne idan har matatar mai ta dangote ta fara tace man da
ya kai ganga dubu 650 kowacce rana.

Yace
matatar man ta dangote da gyaran matatar mai ta Fatakwal zasu zamewa ‘yan Najeriya
rahama a fannin samun rangwamen tsadar farashin mai.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon Gwamnan jihar Kwara Cornelius Adebayo ya rasu yana da shekaru 84

Tsohon Gwamnan jihar Kwara kuma Ministan Sadarwa na baya, Cornelius Adebayo, ya rasu yana da shekara 84 a Abuja da safiyar Laraba nan. Dansa na fari,...

An karrama ma’aikacin gwamnatin Jigawa a Saudiyya bisa dawo da kuɗin da ya tsinta

Wani ma’aikacin gudanarwa a Saudiyya, Muhammed Salalah, ya mika kwafin Alkur’ani Mai Tsarki ga Daraktan Rediyon Jigawa, Malam Isma’il Babura, a matsayin kyauta mai daraja...

Mafi Shahara