DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sabuwar tsadar rayuwa ta tunkaro Nijeriya a 2024

-

Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ta karu da kusan kaso 34 cikin 100 a watan Disambar na shekarar 2023, daga kashi 32.83 da aka samu a watan Nuwamban shekarar ta 2023.

Google search engine

Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta na farashin kayayyaki, na watan Disambar shekarar data gabata 2023, wanda aka fitar a yau Litinin. Hakan ya nuna an samu karuwar kashi 2.72 cikin É—ari, idan aka kwatanta da adadi da aka samu a watan Nuwamba. 

Wannan dai ita ce tsadar abinci mafi muni da aka gani tun shekaru 28 da suka gabata, a cewar wasu majiyoyi. 

Hauhawar farashin ta samo asali ne sakamakon tashin farashin mai da burodi da hatsi da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara