DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotun koli ta kori karar da ke neman a sauke Shugaba Tinubu

-


Google search engine

Kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da aka shigar kan Shugaba Bola Tinubu akan zarge-zargen tu’ammali da miyagun kwayoyi da kuma binciken hukumar leken asiri ta Amurka CIA.

Karar wadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar HDP a shekara ta 2019 Ambrose Aworu ya shigar, ya nemi kotu ta sauke Shugaba Tinubu.

Sai dai a hukuncin kotun mai alkalai biyar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji, ta yi watsi da karar da tace ba ta da tushe kuma ta ci tarar Ambrose Aworu naira miliyan 5. Hakama ta umurci akawun kotun kar ya koma karbar irin wannan karar daga wanda ya shigar da ita Ambrose Aworu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro. Ramaphosa ya...

Sojoji sun ceto mutane shida da aka sace a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar ceto mutane shida da aka sace a wani sumame da suka gudanar a yankunan Kajuru da Kujama...

Mafi Shahara