![]() |
| Kayode Egbetokun |
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan kasar ta samu nasarar kama mutane 30,313, tare da kwato tarin makamai 1,984, da alburusai 23,250 a shekarar 2024 da take bankwana.
Wannan dai na a cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar dake Abuja, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar.
Kayode Egbetokun ya yaba da kwazon jami’an ‘yan sandan na tsawon wannan shekara, musamman irin gagarumar nasarorin da aka samu wajen rage aikata laifuffuka a kasar.




