DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar PCACC a Kano ta zargi tsohon Manajan Daraktan KASCO da karkatar da Naira biliyan hudu

-

 

Google search engine

Hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta zargi tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Kayan Aikin Gona KASCO, Bala Muhammad Inuwa da karbo umurnin kotu ba bisa ka’ida ba domin mayar masa da kadarorin da hukumar ta kwace a binciken da ta ke yi masa na karkatar da Naira biliyan hudu.

A watan Nuwambar shekarar 2023 hukumar ta gurfanar da tsohon Manajan Daraktan da dansa tare da wasu abokanansa bisa zargin karkatar da naira biliyan 4 daga asusun hukumar ta KASCO zuwa wani asusun ajiya na daban.

A firarsa da gidan talabijin na Channels, sakataren hukumar PCACC Zahraddeen Hamisu Kofar-Mata ya ce sun yi mamakin yadda hukuncin kotun ya je ga rundunar ‘yan sanda ba hukumar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Mafi Shahara