DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sufetan ‘yan sandan Nijeriya ya bada umurnin kamo maharan da suka kashe ‘yan sanda a Borno

-

Sufetan ‘yan sandan NIjeriya Kayode Egbetokun ya bayar da umurnin kamo maharan da suka kai hari a ofishin yanki na hedikwatar rundunar dake jihar Borno.
Harin da aka kai a ranar Talata ya yi sanadin mutuwar jami’ai biyu tare da jikkata wani jami’i daya, a lokacin wani musayar wuta da suka yi da maharan wadanda aka ci karfinsu tare da taimakon ‘yan JTF.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ACP Olumiyiwa Adejobi, ya ce Sufetan ‘yan sanda ya yi Allah wadai da harin kuma ya bayar da umurnin kamo maharan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara