DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa ta Nijeriya na son a rage ƙarin kudin kira da na data zuwa kashi 10 ko su tafi kotu

-

Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa ta Nijeriya NATCOMS ta ce za ta dauki matakin shari’a kan hukumar sadarwar Nijeriya NCC, biyo bayan kin amincewar bukatar rage karin kudin kira da data daga kaso 50 zuwa kaso 10.
Yayin zantawarsa da jaridar Punch a ranar Talata, shugaban kungiyar Adeolu Ogunbanjo ya ce halin ko in kula na NCC ya jefa masu amfani da layukan sadarwa cikin zulumi na karin kudaden.
“Mun basu zuwa jiya Talata cewa su fada mana matsayarsu amma har yanzu shiru, ba don haka zamu garzaya zuwa kotu a yau Laraba” in ji Adeolu.
Kungiyar ta NATCOMS na wakiltar al’ummar Nijeriya Miliyan 157 dake amfani da layukan sadarwa daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Baba-Ahmed ya bukaci Tinubu ya fito ya yi ma ‘yan Nijeriya bayani kan barazanar Amurka

Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya fito fili ya yi wa ’yan Nijeriya jawabi...

Sojojin Amurka na jiran umarnin Trump don kai farmaki Nijeriya

Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar da shirin kai farmaki a Nijeriya bayan umarnin tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, bisa zargin...

Mafi Shahara