DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a yanki Arewa sun fara tallata tazarcen shugaba Tinubu a 2027

-

An jiyo wasu manya-manyan jiga-jigan jam’iyyar APC sun fara yakin neman zaben shugaba Tinubu karo na biyu na zaɓen a 2027

Google search engine

Jiga-jigan sun hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje da sakataren gwamnatin tarayya George Akume, sun yi kira ga shugaba Tinubu da ya sake tsayawa takara a karo na biyu.

A kwanakin baya dai shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Ganduje ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da suyi hakuri a zaben 2027 su bai wa shugaba Tinubu ya ida wa’adinsa na biyu.

Shima sakataren gwamnatin tarayya George Akume, yayin da yake magana a wani shirin gidan talabijin na TVC, ya shawarci ’yan Arewa da kada su nemi kujerar shugaban kasa a 2027 su bari sai shekarar 2031.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Trump na Amurka ya amince cewa ba Kiristoci ne kadai ake halakawa a Nijeriya ba

Shugaban Amurka, Donald Trump, a karon farko ya amince cewa ba iya Kiristoci ne matsalar tsaro ta shafa ba, Musulmi ma na daga cikin wadanda...

Wasu lauyoyi biyu daga Tanzania sun yi kara a gaban kotu suna kalubalantar zaɓen 2025 da aka gudanar a kasar

Wasu lauyoyi biyu a Tanzania, Tito Magoti da Bob Wangwe, sun kai ƙasar Tanzania gaban Kotun Gabashin Afirka kan zaɓen da aka gudanar a ranar...

Mafi Shahara