China ta bayyana cewa za ta kara haraji kan kayayyakin Amurka zuwa kashi 125, sai dai za ta yi watsi da wani karin harajin da shugaba Donald Trump zai yi nan gaba.
A cewar ƙasar ta China, ba wani alfanu da zai sa masu shigo da kaya a kasar su sayi daga Amurka, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta sanar da dakatar da harajin da ta sanya wa ƙasashen duniya, yayin da ta kara wa China haraji saboda martanin da ta mayar.


