DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar IHR ta bukaci a yi bitar Hajjin 2025, ta nemi a inganta shirin hajjin 2026

-

Kungiyar da ke sanya ido kan gudanar da aikin hajji da Umrah a Nijeriya, Independent Hajj Reporters (IHR), ta bukaci Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da Hukummomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da su gaggauta gudanar da cikakken nazari kan yadda aikin Hajjin 2025 ya gudana.

A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Muhammed, ya fitar a wannan Lahadi, ƙungiyar ta bukaci a bayyana gaskiyar yadda hajjin 2025 ya gudana domin duba abubuwan da suka faru ba tare da wata rufa-rufa ba. Kungiyar IHR ta ce manufar hakan ita ce kauce wa maimaita kura-kurai da matsalolin da suka faru a bana.

Google search engine

Duk da yabawa da ci-gaban da aka samu a matakin farko na jigilar alhazai da kuma wasu ayyuka a Mina, IHR ta bayyana damuwa kan manyan kura-kurai da suka shafi tsaro da binciken lafiya. Ta bukaci a binciki yadda ‘yan ta’adda da ake nema suka shiga cikin tsarin rijistar alhazai, har aka kama wasu a hanyoyin fita da dawowa daga Saudiyya.

Har ila yau, ƙungiyar ta soki yadda aka gudanar da ayyukan lafiya, tana mai bayar da misalin wata mata mai juna biyu daga Zamfara da ta haihu a lokacin Hajji — lamarin da ta ce ya nuna gazawar tsarin duba lafiyar mahajjata.

kungiyar IHR ta kuma bayyana rashin jin daɗin jinkirin biyan alawus na ma’aikatan wucin gadi a Makkah, da sabanin jadawalin jirage, da kuma karancin gadon kwana a Madina. Ta kuma soki makwancin mahajjata a Makkah da ta ce yana nesa da Masallacin Harami, wanda ya hana mahajjata damar zuwa sallar yau da kullum.

Dangane da Hajjin 2026, IHR ta bukaci NAHCON da ta gaggauta aiwatar da sabon jadawalin Hajj da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar. Kungiyar ta ce wannan jadawalin bai ba da damar jinkiri wajen aiwatar da muhimman ayyuka kamar rajistar mahajjata da shirye-shiryen ayyuka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin kaya zai sauka zuwa kashi ɗaya cikin goma – fadar shugaban Nijeriya

Fadar shugaban kasa ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hauhawar farashin kaya (inflation) a kasar zai ci gaba da sauka, har ya kai zuwa kasa...

’Yan sanda sun kama mutanen da ake zargi da satar kifi a jihar Neja

Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta sanar da kama mutane hudu bisa zargin sata da kuma karɓar kayan sata, bayan da aka sace kifaye da...

Mafi Shahara