Jam’iyyar adawa ta Chadema a Tanzaniya ta bayyana cewa fiye da mutane 700 ne suka mutu cikin kwana uku na zanga-zangar bayan zaɓen shugaban ƙasa, wadda ta haifar da tarzoma da tsaurara matakan tsaro a fadin ƙasar.
A cewar rahoton jaridar Daily Trust, zaɓen ya gudana ne cikin tashin hankali, katsewar intanet da kulle hanyoyin sadarwa, lamarin da ya sa ake diga ayar tambaya kan sahihancin zaɓen da gaskiyar sakamakon.
DCL Hausa ta ruwaito cewa, shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, mai shekara 65, wadda ke neman wa’adin farko cikakke a ƙarƙashin jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM), ta fuskanci hamayya daga ‘yan takara 16. Sai dai hana wasu manyan ‘yan adawa shiga takara da shari’o’in da ke ci gaba, sun jefa shakku cikin tsarin.
Kakakin jam’iyyar Chadema, John Kitoka, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa adadin mutanen da suka mutu a babban birnin kasar, Dar es Salaam ya kai kusan 350, yayin da a a birnin Mwanza ya wuce 200. AFP ya ce jimillar ta kai kusan 700, kuma “na iya ƙaruwa” saboda an kafa dokar hana fita da dare tun ranar Laraba.



